Akwai bukatar Sanata Akpabio ya sauka daga mukaminsa - Jigon APC

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sauka daga kujerar sa saboda zargin yi wa masu zanga-zangar yunwa habaici da ya ce masu zanga zangar na yi su kuma lokacin suna gidajensu suna cin abinci.

Duk da Akpabio ya musanta furta kalaman, a cikin wata sanarwa da ya fitar, Vatsa ya bayyana furucin a matsayin abin kunya ga jam’iyyar mai mulki, inda ya ce Akpabio yana nuna halin kyama irin na jam’iyyar daya fito ta PDP.

Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa da ya baiwa 'yan Najeriya hakuri.

Kazalika Vatsa ya bayyana bawa Akbaio matsayin shugaban majisar dattawa da jam’iyayyar APC mai mulki ta yi a matsayin babban kuskure kuma abin cutarwa ga kasa ya kuma dangantaka hakan da dalilin rashin samun nasarar gwamnatin .

1 Comments

Previous Post Next Post