Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa wasu matasa sun bazama kan titunan jihar Neja domin nuna adawa da matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.
Matasan dai suna ɗauke ne da kwalaye da aka rubuta sakonni daban-daban wadanda ke cewa " ya isa haka, dole a dakatar da tsare-tsare masu musguna wa talakawa, ba za mu zama bayi a ƙasar mu ba, dole a mayar da tallafin man fetur"
Bayan kasancewar su ɗauke kwalayen masu rubuce-rubuce, matasan suna kuma wake-wake da ke nuna adawa da gwamnati.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan da gwamnan jihar ta Niger Mohammed Bago ya yi alkawarin baiwa ma'aikata ƙarin Naira dubu 20 baya ga albsahin su dan rage radadain tsadar rayuwa, ya kuma bayar da umurnin a fitar da tan 500,000 na abinci domin saida shi ga jama'a a farashi mai rabuwa a jihar.