Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa za a warware matsalolin da zasu sa a gudanar da zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.
Wasu kungiyoyi da daidaikun jama’a ne zasu gudanar da zanga-zangar a fadin kasar a ranar 1 ga watan Agusta domin kawo karshen tsadar rayuwa a kasar.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a ranar Laraba ya yi wata ganawar sirri da ministoci kan baton.
Da yake jawabi bayan taron, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce babu wanda zai bacci a tsakaninsu har sai an warware matsalolin.
Idris ya ce gwamnati ta kasance tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki da sauran masu shirya zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.