Zanga-zanga ba zata magance kalubalen dake Nijeriya ba– Gwamna Namadi

Zanga-zanga ba zata magance kalubalen dake Nijeriya ba– Gwamna Namadi

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ranar ya ce zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar a ranar 1 ga watan Agusta, ba ita ce mafita ga kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu ba.


Gwamnan ya bayyana hakanne a wani taro da aka yi da kungiyoyi 27 da ya gudana ranar litinin a birnin Dutse.


Namadi yace tabbas Nijeriya na fama da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tabbas


Amma, zanga-zangar ba ita ce mafita ba. Akwai hanyoyi da dama da mutane za su iya bayyana kokensu, mutane suna da 'yancin nuna korafe-korafensu ta hanyar zanga-zangar karkashin mulkin dimokradiyya, amma wannan ba ita ce hanya mafi inganci don magance matsalolin ba.


Yace zanga-zanga kadai ba za ta samar da mafita ba, jama’a su koma ga Allah, su tuba, su nemi gafara da sa hannun Ubangiji kan kalubalen da kasa ke ciki.


Namadi ya ce gwamnati ta yi iyakacin kokarinta ta fuskar samar da kayan abinci da sauran kayayyaki da suka hada da raba kudade domin rage wahalhalun da jama'a suke fuskanta a dukkan matakan gwamnati.


Gwamnan ya kuma tunatar da jama’a cewa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta amince da shigo da kayan abinci cikin kasar na tsawon watanni biyar ba tare da harajin shigo da kaya daga kasashen waje ba.


Namadi ya shawarci ‘yan Nijeriya da su yarda da wahalhalu a matsayin jarabawa daga Allah, ya kara da cewa kowane musulmi yasan kaddara ko mai kyau ko mara kyau don haka al'umma su cigaba da addu'ar samun sauki ga kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp