Za a rika ba mata hutun 'ta-kaba' idan mazajensu sun rasu a Katsina
Gwamnatin jihar ta bullo da sabon tsarin ba mata ma'aikatan da mazajensu suka rasu hutun watanni hudu da kwanaki 10 don su yi 'ta-kaba' a jihar.
Musulunci dai ya tanadi 'ta-kaba' ga matan da mazajensu suka rasu su zauna gida a killace don jimamin rasuwar mazajen nasu.
Jaridar Punch ta jiyo shugaban ma'aikatan gwamnati a jihar Katsina Falalu Bawale ba cewa an aike da sanarwa ga duk ma'aikatu, sassa da hukumomin gwamnati da su rika ba mata hutun 'ta-kaba' idan mazajensu sun rasu.
Hakan dai ya biyo bayan bukatar da majalisar dokokin jihar ta gabatar na neman a samar da tsarin ba da hutun 'idda' ga mata ma'aikatan da mazajensu suka rasu, wanda daga bisani sashen zartarwar jihar ya amince.