Hukumar zabe ta jihar Kano tace za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar ranar 30,ga watan Nuwambar shekarar 2024.
Shugaban hukumar zaben na jihar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau laraba.
Yace hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan kananan hukumomi da kansiloli,kuma tuni shirye shirye sunyi nisa domin kuma tuni suka aikawa jam'iyyu da ranar da zasu fara sayar da fama famai domin da kuma ranar da zasu maidoshi domin cigaba da tantance 'yan takarkaru.