Yanzu lokaci ne da zamu magance matsaloli bawai zanga-zanga ba -Kashim Shettima

Yanzu lokaci ne da zamu magance matsaloli bawai zanga-zanga ba -Kashim Shettima


Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima,yanzu lokaci ne da za a magance matsaloli ba wai zanga-zanga ba,ya bayyana hakan ne a yayin wani babban taro a fadar shugaban kasa da ke Abuja.


Shettima ya jaddada bukatar daukar kwararan matakai kan zanga-zangar duk da cewa ya amince da wahalhalun da 'yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da aka yi a baya-bayan nan, musamman cire tallafin man fetur.


An bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasar kan kafafen yada labarai Stanley Nkwocha ya fitar.


Yace wannan lokaci ne da ya kamata mu magance matsalolinmu, ba wai yin zanga-zanga ba. Kowa nada ‘yancin gudanar da zanga-zanga a yawan kasashen dimokuradiyya da ake a duniya,amma wasu na kokarin tada zaune tsaye da ba a san inda za a kawo karshensa ba.


"Ina so in yi kira gare ku da ku ba da shawarwari irin na diflomasiyya, haɗin da karin karfin gwiwa, da haƙuri,shugaban mu ya na aiki sossai wajen inganta abubuwa a Nijeriya"

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp