'Yan sanda a jihar Legas sun cafke wani barawo da ya ba direban Uber farfesu ya nemi ya sace masa motarsa

 'Yan sanda a jihar Legas sun cafke wani barawo da ya ba direban Uber farfesu ya nemi ya sace masa motarsa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, a ranar Asabar din dinnan ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da satar mota kirar Uber bayan ya lallabi direban da ya bashi farfesu.


Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ranar Asabar.


Mista Hundeyin ya ce, rundunar ‘yan sandan Akinpelu ta samu rahoto a ranar 5 ga watan Yuli da misalin karfe 8:00 na dare daga wani direban Uber, wanda ba a ambaci sunansa ba.


Ya ce direban motar ya ba da rahoton cewa ya dauko fasinja, wanda kawai ya bayyana sunansa da Ishaya, daga gidan man NNPC, Maryland, a cikin motarsa Toyota Corolla zuwa wani otal da ke unguwar Oshodi.


Kakakin ya yi nuni da cewa, a otal din, wanda ake zargin ya saya wa direban abinci, da farantin miya da nama da kuma abin sha guda daya.


A cikin haka ne, lokacin da wanda ake zargin ke neman abinda zai wanke hannunsa, direban ya ba shi makullin motarsa ya yi amfani da shi daga nan ya arce da motar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp