'Yan jaridar da aka yi garkuwa da su a Kaduna sun kubuta
'Yan jaridar da akayi garkuwa dasu a kaduna na jaridar The Nation, Alhaji AbdulGafar Alabelewe, da na jaridar Blueprint, AbdulRaheem Aodu, tare da iyalin su sun samu 'yanci.
An yi garkuwa da ‘yan jaridan tare da iyalin su daga gidajensu ne a unguwar Danhonu da ke garin Millennium na karamar hukumar Chikun a Kaduna, a ranar 7 ga Yuli, 2024.
Daga baya ‘yan bindigan suka fara sako matar Abdulraheem.
Da yake tabbatar da sakin su, 'yayan Abdulgafar, Barista Mas’ud Mobolaji Alabelewe, ya ce bayan sako su suna asibiti a Abuja domin karbar magani.