'Yan bindiga sun yi mummunan ta'adi a kauyen jihar Zamfara
Wasu ‘yan bindiga sun halaka mutane hudu tare da sace wasu 150 ciki har da jarirai biyu ‘yan shekaru shida da watanni takwas a wani hari da suka kai kauyen Dan Isa da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara ranar Lahadi.
Dan Isa dai tana kasa da kilomita 14 daga Gusau, babban birnin jihar.
Harin dai ya faru ne mako guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka sako mazauna garin Dogon Kade su 46, biyo bayan zargin biyan naira miliyan 21 na kudin fansa.
Wani mazaunin garin Dan Isan da aka sace matarsa da dansa ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.
Mazaunan wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Lahadi, inda suka shafe sa’o’i shida suna gudanar da barna a yankin.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun zo ne a kan babura kusan 150, kowannensu na dauke da mutane uku, inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba, lamarin da ya sa mazauna yankin tserewa domin tsira da rayukansu.
Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, ya ce ‘yan sandan ba su samu labarin faruwar lamarin ba.
Sai dai ya tabbatar da wasu hare-hare guda biyar a Gusau a makon jiya, inda aka yi garkuwa da mutane 11.