‘Yan bindiga sun saka harajin kusan N200m a wasu al’ummomi a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Jaridar Daily Truth ta ruwaito Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Yan Dolen Kaura: Naira miliyan 15; Gidan Zagi: Naira miliyan 15; Million Kanwa: Naira miliyan 20; Kaiwa Lamba: Naira miliyan 26; Gidan Dan Zara: Naira miliyan 22; Jinkirawa: Naira miliyan 16; Dumfawa: Naira miliyan 16; Ruguje: Naira miliyan 7; Babani: Naira miliyan uku da Gidan Duwa: Naira miliyan hudu.
An bayyana cewa wasu kauyukan sun riga sun biya kudaden harajin nasu, yayin da wasu kuma ke fafutukar tattara kudaden da ake bukata.
Wannan lamarin, in ji majiyoyi, ya tilasta wa mazauna kauyukan neman aikin yi a garuruwan da ke kusa da su, don tara kudaden domin biyan bukatun ‘yan fashin.
Wani mazaunin garin Zurmi mai suna Malam Yunusa Musa ya shaida wa Daily Truth cewa harajin ya fara aiki daga wannan makon.