Wike ya ba da sharudda ga masu shirin yin zanga-zanga a Abuja
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana sharudda ga wasu ‘yan Nijeriya da ke son yin amfani da dandalin Eagle Square domin gudanar da zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agusta a fadin kasar.
Wike ya bayar da sharuddan ne yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da aka yi a Abuja ranar Asabar, domin hana mazauna babban birnin tarayya shiga zanga-zangar da za'ayi a fadin kasar.
Ya bayyana cewa taron ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki a babban birnin tarayya Abuja su amince da bukatar zaman lafiya, wanda ba za a iya tabbatar da shi ba, idan mazauna yankin suka shiga zanga-zangar.
Yace wadanda suke son yin zanga-zangar, sun nemi ya basu filin Eagle Square domin su gudanar a wajen.
Wike ya ce dole ne sai sun rubuta wasika gareshi,kuma yasan su wanene zasu yi sannan kwana nawa zasu dauka kafin su gama.
"Amma ba'asan ko su wanene ba sedai kawai a jisu a kafafen yada labarai suna bayyana zasu yi zanga-zanga,"ba kawai mun hana su bane dole ne su cika sharuddan"
Ya kara da cewa "ba ina cewa kada mutane su yi zanga-zanga ba,babban birnin tarayya Abuja wuri ne na zaman lafiya da ya hada al'umomi da dama,don haka baza mu bari a yi tashe-tashen hankula a cikin rigar zanga-zanga ba.