Wata makaranta ta rufta lokacin da dalibai ke tsaka da rubuta jarrabawa a Jos
Dalibai dama sun makale a wata makaranta da ta rufta a unguwar Busa Buji dake karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
A cewar shaidun gani da ido, ginin gidan, Saint Academy ya rufta ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Juma’ar nan, inda daliban da ke rubuta jarabawa suka makale.
Bayan samun labarin rugujewar ya, iyaye da dama sun yi tururuwar zuwa makarantar suna domin dauka 'yayansu.
Har zuwa wannan lokaci ana ci gaba da aikin ceto daliban, kuma jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun isa wurin domin ceto daliban da suka makale.