Kungiyar Gwamnonin Nijeriya na jam'iyyar PDP ta yi la'akarin cewa 'yan kasar na cikin matsin rayuwa da ya jefa su cikin talaucin da ke gasa musu aya ga hannu.
Kungiyar ta yi zargin cewa wannan matsin rayuwa da wasu 'yan Nijeriya ke ciki ya faru ne ta dalilin barnatar da dukiyar kasa da gwamnatin jam'iyyar APC ke cikin yi.
A cikin wata sanarwar bayan taron da suka gudanar a Enugu, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Gwamnan Bauchi Bala Muhammad, kungiyar ta ce jam'iyyar APC ta wargaza duk wani cigaba da jam'iyyar PDP ta kafa cikin shekaru 16 da ta yi tana jagorantar kasar.
Gwamnonin na jam'iyyar PDP suka tunaso yadda suka ce 'yan Nijeriya na warwasawa a zamanin PDP na mulki da yadda take kula da talakawa ta hanyar dakile duk wani yunkurin hauhawar farashi.