Tinubu zai halarci taron hadin kan kasashen Afrika a Ghana
A ranar Asabar din nan ne shugaba Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Accra na kasar Ghana domin halartar taron koli na tsakiyar shekara na kungiyar tarayyar Afirka (AU) karo na shida.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan al'umma, Ajuri Ngelele ya fitar ta ce, shugaba Tinubu zai yi jawabi a taron kan matsayin hadin kan yankin a sassa daban-daban na Afirka, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da aka fuskanta a yammacin Afirka tun bayan ganawar karshe da aka yi a Nairobi, Kenya, a watan Yuli shekarar 2023.
Shugaba Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, zai gabatar da ‘Rahoto na 2024 game da halin da al’umma ke ciki, wanda zai mai da hankali kan zaman lafiya, tsaro na yankin Afrika, da gudanar da mulki.