Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa Trump

Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa Trump

Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.


An kai harin ne ga Trump a wani gangamin siyasa a ranar Asabar, Yuli 13, 2024, a Pennsylvania, Amurka.


Trump ya tsallake rijiya da baya, yana mai cewa, An harbe shi ne da harsashi wanda ya huda saman kunnen sa na dama.


Hukumar bincike ta FBI ta bayyana cewa Thomas Crooks mai shekaru 20 ya yi harbin bindigar, inda ya halaka mutum daya yayin da wasu biyu suka samu raunuka.


Sai dai kuma a cewar wata sanarwa da Tinubu ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, ya ce harin da aka kai wa Trump abin kyama ne kuma ya wuce ka’idojin dimokradiyya.


Shugaban na Nijeriya ya tabbatar da cewa tashe-tashen hankula ba su da gurbi a dimokuradiyya, ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga tsohon shugaban na Amurka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp