Ta akwatin zabe ya kamata 'yan Nijeriya su nuna fushinsu ba ta hanyar zanga-zanga ba - Kwankwaso
Jagoran jam’iyyar (NNPP) na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su nemi sauyi ta hanyar dimokradiyya maimakon zanga-zanga.
A wata sanarwa da ya sanyawa hannu,Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa za a iya samun sauyi mai inganci kuma mai dorewa ta hanyar karfin yin zabe.
Yace mun tsinci kanmu cikin wahalhalun da ba za a iya misaltawa ba saboda shugabanninmu sun rasa wasu abubuwa.
“Duk da haka, a ko da yaushe akwai damar yin gyara da dora kasar nan kan turba mai kyau don bunkasar tattalin arziki, wadata, da kyautata jin dadin ‘yan kasa.
Kwankwaso ya bayyana wasu rigingimu da suka samo asali daga rashin shugabanci na gari, kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi katsalandan a harkokin masarautun jihar Kano, da tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, da rudanin siyasa a jihar Ribas, da rashin tsaro.
Ya kara da cewa wadannan al’amura alamu ne na rashin bin ka’ida da kuma nuna gaskiya ga Shugabanin a Nijeriya.
Ya yi kira ga shugabannin Nijeriya a dukkan matakai da su gaggauta magance wadannan kalubale ta hanyar tabbatar da kyakkyawan shugabanci da bin doka da oda.