Sudan ta ayyana dokar ta baci, tare da bai bakin haure wa'adin ficewa daga kasar

Sudan ta ayyana dokar ta baci, tare da bai bakin haure wa'adin ficewa daga kasar

Gwamnan Khartoum, Ahmed Hamza, ya ba da wa'adin kwanaki 15 ga baki 'yan kasashen waje su fice daga babban birnin kasar Sudan da kewaye daga ranar Juma'a 12 ga Yuli 2024.


A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Sudan da ke Nijeriya ya fitar a karshen makon nan, gwamnan ya ce umarnin da aka ba wa 'yan kasashen wajen na ficewa daga Sudan an tsara shi ne domin magance matsalar rashin tsaro a kasar.


Sanarwar ta ce, bisa shawarar kwamitin kula da harkokin tsaro na birnin Khartoum aka bada wannan umurni.


Hukumomin jihar sun baiwa baki wa'adin ficewa daga jihar bisa la'akarin rashin tsaro daya ta azzara a yankin. Jihar Khartoum ta tsawaita wa'adin kwanaki 15 kacal ga baki 'yan kasashen waje su fice daga jihar, bisa shawarar da kwamitin tsaro ya yanke.


Kwamitin ya gudanar da wani taro don bin diddigin aiwatar da dokar hana fita da babura a yankin kamar yadda sanarwar ta shaida.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp