Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya na bukatar Majalisar dattawa ta ƙasar ta sake aiki kan kasafin kudin bana, ta yadda za'a ƙãra wasu Naira tiriliyan shida a kasafin kudin na shekarar 2024.
Tanubu ya nemi ayi wannan ƙari ne a bangarori biyu na kasafin kudin, wato ɓangaren kuɗaɗen gudanarwa da kuma na manyan ayyuka waɗanada kowannen su za'a yi ƙãrin Naira tiriliyan uku uku.
A wasikar da ya aike ga majalisar shugaba Tinubu ya ce za'a ciri wadannan kuɗaɗen ne daga kudin haraji da ake tarawa.
Tuni majalisar ta rubuta wannan bukata cikin jerin batutuwa da zata yi zama kansu.
Idan majalisar ta amince da wannan buƙata ta shugaba Tinubu dai kasafin kudin na shekarar 2024 zai tashi daga sama da Naira tiriliyan 27 zuwa sama da Naira tiriliyan 33.