Wani makusancin ministan gidaje a Nijeriya Arch Ahmad Musa Dangiwa ya sanar cewa babu kanshin gaskiya a zargin da ake yi cewa shinkafar da jami'an DSS suka sanar da kamawa a Katsina, ta ministan ce da gwamnatin tarayya ta bashi a rarraba a jihar Katsina.
Salisu Hamza Rimaye a cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina ya ce an jawo hankalinsu akan wani rahoto da ake zargin karkatar da kayan abinci da Gwamnatin tarayya ta bayar da nufin rabawa a jihar Katsina daga wajen Minista Dangiwa.
Rahoton ya yi ikirari cewa wani na kusa da ministan gidaje da raya birane Arc. Ahmed Musa Dangiwa ne ya karkatar da wannan kayan abinci.
Salisu Hamza ya sanar cewa babu kamshin gaskiya a kan wadannan zarge-zargen. Wannan ikirari rashin fahimta ne kawai daga wadanda su ka bayar da rahoton.
Ya kara da cewa Minista, Dangiwa wanda ya yi fice wajen taimakon jama’a, yana da tarihin rikon amana da karimci.
"Sama da shekaru goma yana raba wa al'umma daruruwan ton-ton na kayan abinci musamman a lokutan azumin Ramadan da sauran lokutan bukukuwan sallah da makamantansu". In ji shi.
Ya ci gaba yana cewa malaman addini, shugabannin jam’iyya, da marasa galihu da sauran al'umma duk sun kasance masu amfana da ire, iren wadannan kayakin abinci da Ministan yake rabawa duk shekara.
Makusancin ministan ya ce wadannan zarge-zargen da ba su da tushe balle makama. Ya kara da cewa illa ce ga kokarin da Ministan ke yi na tallafa ma al’umma.
Ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da wannan ikirari maras tushe.
Sannan ya sanar da Jama'a cewa kayaki na nan, nan gaba kadan bayan an gama tsare-tsaren da shirye, shiryen raba su za a kira taro a raba.