Obi ya yi tir da koma bayan da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa

Obi ya yi tir da koma bayan da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda tattalin arzikin kasar ke tafiya tun daga shekarar 2015.


A cikin wata sanarwa a ranar Litinin dinnan daya fitar ta shafinsa na X, Obi ya bayyana bambancin da ke tsakanin yadda tattalin arzikin Nijeriya ya samu a farkon shekarun da ta dawo kan tafarkin dimokuradiyya da kuma halin da take ciki yanzu.


Yace lokacin da Nijeriya ta koma kan mulkin dimokuradiyya a 1999, ta ci gaba da samun karuwar GDP da kusan kashi 6.72 cikin dari na tsawon shekaru 16 daga 1999 zuwa 2014.


Yace duk da cewa, wannan ci gaban bai dore ba, inda karuwar GDP ta ragu zuwa kashi 2.79 cikin 100 a shekarar 2015, sannan kuma tattalin arzikin kasar ya shiga cikin koma baya a shekarar 2016.


A shekarar 2014, gabanin kafa sabuwar gwamnati shekara guda, Nijeriya ce ta fi kowacce kasa karfin tattalin arziki a Afirka inda ta samu babban arzikin cikin gida da ya kai dalar Amurka biliyan 568.5.


Sabanin haka, ya yi nuni da cewa, ya zuwa shekarar 2023, Nijeriya ta fada cikin kasa ta 4 mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, inda ta samu GDP da ya kai dala biliyan 375.


Don haka, lamarin ya kara tabarbarewa a shekarar 2024, inda GDP ya kara raguwa zuwa kimanin dala biliyan 253.


Wannan ya kasance bisa ga bayanan da aka samu daga StatiSense, wani kamfani na AI wanda ya ƙware a nazarin rahoton kuɗi da kimanta bayanan banki.


Daga bisani,Peter Obi ya nuna bacin ransa kan yadda al’amura ke tafiya, inda ya ce, a yau, talauci ya yi kamari, kuma sai karuwa yake yi. rashin aikin yi na karuwa,farashin kayan abinci ya karu sama da kashi 43%.


Ya ce, ya kamata a dauki matakan gaggawa domin ceto al’ummar kasar daga durkushewar tattalin arziki da kuma fitar da ita daga cikin yunwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp