Za a inganta alaka tsakanin Nijeriya da Masar
Jakadan Masar a Nijeriya, Mohamed Fouad, ya bayyana cewa Nijeriya da Masar na fatan inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.
Fouad ya ce, a shekarar 2023, yawan ciniki tsakanin kasashen ya kai dalar Amurka miliyan 190.
Jakadan ya bayyana mamakinsa kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu take, yana mai cewa da gangan ana kokarin sanya gaba a tsakani.
Ya ce akwai manyan tsare-tsare guda biyu a wani bangare na kokarin kyautata huldar dake tsakanin Nijeriya da Masar.
Jakadan ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin bikin cika shekaru 72 da juyin juya halin kasarsa a watan Yuli.
Yace a matsayin mu na manyan kasashe a Afrika,dole mu kyautata alaka a tsakani ta yadda al'ummar mu zasu amfani kwancen.
Ya kara da cewa, a yau, Masar da sauran kasashen Afirka suna kokarin ganin sun magance kalubalen dake gabansu wadanda suka fuskanta a lokacin gwagwarmayar neman ‘yancin kai.
Don haka Nijeriya da Masar na da bukatar karfafa alaka ta hanyar cinikayya da sauran dabarun tattalin arziki.