MUNA TARE DA MATASAN MU
Wannan sanarwar ce ga manema labaru a kan zanga-zangar da ake shirin yi, da aka fitar da ita a ranar 31 ga watan Yuli wadda dattajan arewacin Najeriya da suka hada da Professor Usman Yusuf da Naja’atu Muhammad da Malam Salihu Lukman da Dr. Ardo Umar suka fitar a birnin Abuja.
-------
Mu dattawan Arewa kuma ginshikai da ke da ruwa da tsaki a ƙasar nan muka yi wannan rubutu domin tsayar da matsaya a kan babban lamari da ya shafe mu duka.
Kamar yadda kuka sani, ƙasarmu ta dade
tana fama da matsaloli ba 'yan kaɗan ba ɓangaren rashin tsaro, da tsananin
talauci, da tsananin yunwa da jahilci da
rashin aikin yi, da cututtuka da tsananin tsadar rayuwa, da duk rashin
shugabanci na gari da rashawa a ofisoshi ne gwamnati suka haddasa su.
Muna sane cewa babbar manufar dukkan
wata gwamnati ita ce kare rayuka da dukiyar jama'a da kyautata jin dadin
al'ummar kasa. Duk gwamnatin da ba ta
iya samar wa al'ummarta wadannan muhimman haƙƙoƙi nasu to ta rasa huruminta na
ci gaba da kasancewa a madafun iko, kuma ko shakka babu za ta gamu da fushin
'yan ƙasa. Saboda haka za ta iya ci gaba da kasancewa a kan mulki ne ba da fatan
alheri daga jama'a ba.
Da alama yanayin da ake ciki ke nan a
Najeriya, inda ƙasarmu, abar ƙaunarmu Nijeriya, ta dosa ke nan.
Shekaru da dama gwamnatocin da suka
gabata a dukkan matakai, ciki har da gwamnatoci da ke ci a yanzu, sun gaza
samar da shugabancin da ake buƙata.
Saboda haka aka jefa 'yan Nijeriya cikin
mawuyacin hali, na rashin sanin inda rayuwarsu ta dosa, ga ƙunci da sauransu
musamman matasa.
Domin matasa su bayyana buƙatunsu kan
tsadar rayuwa, da matsalar tsaro, da lalacewar lamura, suka sa matasan Nijeriya
suka yanke shawarar gudanar da zanga-zanga ta ƙasa baki-ɗaya daga 1 zuwa 10 ga
watan Agusta.
Saboda
haka muka rubuta wannan sanarwa ta musamman domin bayyana matsayinmu a game da
wannan zanga-zanga da matasa suka tsara da kuma halin da gwamnati take nunawa a
kan zanga-zangar.
Da farko muna so mu jaddada kariyar da
tsarin mulki ya ba kowanne ɗan ƙasa a 'yancin da yake da shi na yin taro da
kuma yin zanga-zanga.
Har ila yau muna jaddada cewa dalilan da
suka haddasa zanga-zangar dalilai ne masu ƙwari.
Saboda haka muke bayyanawa ɓaro-ɓaro
cewa muna tare da matasanmu a wannan gwagwarmaya tasu ta aiki da 'yancin da
suke da shi na gudanar da zanga-zanga.
Na biyu muna kira ga gwamnatin tarayya
ta zama mai sanin ya kamata wajen warware wannan matsala idan har tana so ta
warware cikin ruwan sanyi da kauce wa dukkan wata matsala da ke tattare da
gagarumar zanga-zanga. Saboda haka muke ba gwamnati shawarar ta hanzarta ɗaukar
waɗannan matakan:
1. Tattaunawa: Gano shugabannin matasan da
masu zanga-zangar tare da ganawa da su kai tsaye domin fahimtar
ƙorafe-ƙorafensu da kuma magance musu su. Ɗora wa wasu wannan aiki kamar irin
su sarakuna, da shugabannin addini, da shugabannin kwadago da na farar hula ba
zai yi aiki ba.
Amfani da ƙarfin tuwo wajen tursasa wa
masu zanga-zangar zai ƙara sa yanayin da ake ciki ya ƙara ta'azzara ne. Mun dai
ga yadda zanga-zangar EndSARS ta wanye.
2. Aiwatar da sauye-sauye: A duba
buƙatun masu zanga-zangar tsakani da Allah ta hanyar aiwatar da sauye-sauye
masu ma'ana, da nuna fata ta gari da dukufa ga canji.
3. Ba da goyon baya ga karfafa matasa: A
zuba jari ga tsare-tsare na ci gaban matasa, da iliminsu da dabaru na bunƙasa
kasuwancinsu.
4. Bunƙasa ci gaban tattalin arziki:
Aiwatar da tsare-tsare da za su kyautata ilahirin ci-gaban tattalin arzikin
ƙasa.
5. Kyautata shugabanci: Gaskiya da riƙon
amana da damawa da kowa a sha'anin shugabanci, maimakon shugabanci na son- kai
da-baba-kere, da magance rashawa da tabbatar da dama iri guda ga dukkan 'yan
ƙasa.
6. Tabbatar da tsaro: A tabbatar da
jami'an tsaro na ƙasa sun mutunta 'yancin da masu zanga-zangar suke da shi ta
hanyar ƙyale su, su gudanar da taronsu cikin ruwan sanyi ba tare da musu
katsalandan ba, ko tursasa musu ko cin zarafinsu ba, tare da kare su daga
dukkan wata illa ko rauni.
7. Shugabanci abin koyi: Ya kamata
gwamnati da shugabanninta su nuna shugabanci abin koyi, nuna sadaukar da kai,
da kima, da martaba domin cusa ƙauna da amincewa.
A
matsayinsa na wanda shi da kansa ya jagoranci zanga-zanga daban-daban daga
lokacin kungiyar NADECO zuwa shekara ta 2014, Shugaba Tinubu ya fi kowa sanin
darajar zanga-zanga.
Ga
su kuma matasa masu zanga-zanga, muna so mu tabbatar muku cewa mun fahimta tare
da ba da goyon bayan wannan shawara da kuka yanke ta aiki da 'yancin da kundin
tsarin mulki ya ba ku ta gudanar da zanga-zanga ta lumana domin neman
shugabanci na gari da gaskiya daga shugabanku.
Mun yi imanin cewa wannan mataki ne
halastacce kuma matakin da ya wajaba domin kyautata alƙiblarku da tabbatar da
Nijeriya ta mana daɗi gaba ɗayanmu.
A matsayinmu na dattawa, a lokacin da
muke tafiya kafaɗa-da-kafada da ku a kan wannan, muna kira a gare ku, ku ci
gaba da kasancewa masu zaman lafiya da kiyaye doka a lokacin wannan
zanga-zanga, da kauce wa dukkan wani abu da zai iya zamewa tashin hankali, ko
illa, ko ɓarna ko barazana ga zaman lafiya.
Har ila yau muna kira gare ku, ku amince
da tattaunawa idan gwamnati ta nemi yin haka da ku wajen magance ainihin
musabbabin ɓacin ranku.
Ta hanyar ɗaukar waɗannan matakai,
gwamnati tana iya magance waɗannan matsaloli da suka yi sanadiyyar
zanga-zangar, da rage zaman ɗar-ɗar da samar da kyakkyawar makoma da kauce wa
dukkan wata tashin-tashina.
Muna kira ga shugabanninmu da gwamnatoci
a kowanne mataki su zama masu sauraren koke-koken jama'a, su kuma mutunta 'yancin kowanne ɗan ƙasa na bayyana
ra'ayinsa ba tare da wata tsangwama ba, kamar yadda kundin tsarin mulki na
shekarar 1999 ya tanadar.
Mun yi imanin cewa idan muka hada ƙarfi,
za mu iya samar da ƙasa da za ta yi wa kowa daɗi, ba tare da wani bambanci na
shekara, ko ƙabila, ko matsayi na zamantakewa da tattalin arziki ba.
Muna
godiya. Sakonmu
ke nan a yau, mune naku
Farfesa Usman Yusuf da Hajiya Naja'atu Muhammad
Da
Malam Salihu Lukman da kuma Dakta Umar Ardo