Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar kuma madagun adawa a Kasar ya yaba hukuncin kotun koli da ya baiwa kananan hukumomin ƙasar ikon sarrafa kuɗaɗen su ba tare da an hada su da gwamnoni ba.
Atiku, a shafin sa na twitter, ya ce wannan mataki na kotun ƙoli nasara ce ga yan Najeriya kuma abin a yaba ne matuka saboda ya kawar da mummunan tsarin nan da gwamnatocin jihohi ke amfani da shi suna sakaye kuɗaɗen ƙananan hukumomi a asusun gwamnatin jiha.
Madugun adawan na Najeriya yayi fatan yancin na kananan hukumomi zai zarta ɓangaren kudi kadai, yana bayar da shawarar a raba su da jihohi kuma wurin karbar Barack da tara shi saboda yadda ya ce gwamnatocin jihohi ke yin yadda suka ga dama da kuɗin haraji na kananan hukumomi.