Na janye daga takarar shugaban kasa don bawa masu tasowa dama-Jeo Biden
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana dalilin da ya sa ya ki tsayawa takara a babban zaben kasar dake tafe a watan Nuwamba.
Biden, mai shekaru 81, ya yi aiki a matsayin mataimakin Barack Obama, a lokacin da ya yi wa'adi biyu a matsayin shugaban kasad Amurka.
Kamar Obama da sauran 'yan jam'iyyar Democrat, Biden ya bi sahun Hillary Clinton a zaben shugaban kasa na 2016 da Shugaba Donald Trump ya lashe.
Shekaru hudu bayan haka, Biden ya doke Trump wanda ke neman sake tsayawa takara. Sannan ya yi shekaru 77,inda ya kafa tarihi a matsayin mutum mafi tsufa da aka zaba.
Duk da haka, shugabancinsa ya yi ta fama da cece-kuce, musamman saboda rashin lafiya da ya yi fama da ita.
Yayin da yake bayyana matakinsa na yin murabus, Biden ya ce zai ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban kasa da kuma babban kwamandan rundunar har sai wa'adinsa ya kare a watan Janairun 2025.
Da yake magana a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin a daren Laraba, Biden ya ce ya kawo karshen yakin neman zabensa na sake tsayawa takara a wani yunkuri na ceto demokradiyyar Amurka.
A cewarsa, ya amince da mataimakiyarsa, Kamala Harris, don hada kan 'yan uwansu na Democrat da kuma kasar baki daya.
Ya ce ina girmama wannan ofishin, amma ina son kasata,shiyasa na yanke shawarar hanya mafi dacewa domin samun nasara.