Na dade ina mafarkin za ma dan wasan Real Madrid-Kylian Mbappe

Na dade ina mafarkin za ma dan wasan Real Madrid-Kylian Mbappe


Kylian Mbappe ya ce burinsa na komawa Real Madrid a lokacin yaro ya cika yayin da aka bayyana shi a filin wasa na Bernabeu mallakin Real Madrid.


Dan wasan na Faransa, mai shekara 25, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a kungiyar a watan Yuli bayan karewar kwantiraginsa na Paris St-Germain ta kasar Faransa.



Da yake magana a gaban magoya bayan kungiyar sama da 80,000 a Bernabeu, Mbappe ya shaida wa magoya bayansa cewa ya yi mafarkin lokacin da zai iya kiran kansa dan wasan Real Madrid.


Mbappe ya ce ,na shafe dare da yawa ina mafarkin wata rana ina buga wa Real Madrid wasa kuma a yau ina farin ciki ba iyaka


Rana ce mai ban mamaki a gare ni, na yi mafarkin wannan rana tun ina yaro kuma bazan taba mantawa ba


Mbappe, wanda aka saka a cikin sabuwar kayan gida na kulob din kuma ya yi jawabi ga 'yan kallo cikin harshen Sipaniya, shugaban kulob din Florentino Perez ya gabatar da shi ga jama'a.


Da yake magana da Mbappe kafin Bafaranshen yayi magana da jama'a, Perez ya ce: "Ƙaunar da kuka yi wa Real Madrid, kuma kun kasance tare da wannan kulob ɗin tun kuruciyar ku, ya ba ku damar kasancewa a nan kuma ku shawo kan waɗannan matsalolin a hanya. ga mafarkinka."

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp