Matatar man Dangote ba zata fasa aiki ba- Kwankwaso ya fadawa gwamnatin Nijeriya

Matatar man Dangote ba zata fasa aiki ba- Kwankwaso ya fadawa gwamnatin Nijeriya

Dan takarar shugaban kasa a (NNPP) a zaben 2023 kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, ya mayar da martani kan takaddamar da ke tsakanin matatar man Dangote, da masu kula da bangaren mai a Nijeriya.


A makonnin da suka gabata ne dai Dangote da hukumomin a Nijeriya ke takun-saka game da matatar mai da ke yankin Ibeju-Lekki a jihar Legas.


Ya kai wani sabon mataki a lokacin da hukumar kula da man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce har yanzu gwamnati ba ta ba da lasisin fara aiki ba ga matatar man Dangote.


Sai dai a wani mataki na warware matsalolin, karamin ministan albarkatun man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren mai da iskar gas sun gana da Dangote a ranar litinin.


A wani sako ta hanyar X a ranar Laraba, Kwankwaso ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta tabbatar da nasarar aikin matatar man ta Dangote.


Yayin da yake bayyana ra'ayinshi Kwankwaso ya ce dole ne gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta nuna adalci ga irin wannan gagarumin aiki da Dangote ya dauko domin samun nasarar sa.


Yace na yi farin ciki da ziyartar matatar mai ta Dangote, kuma na yi mamakin irin jajircewar da aka yi wajen ganin an kafa ta.


Lokaci ya yi da za mu hada kan wannan kadarorin kasa don ganin cewa babban aikin ba'a samu matsala ba, kuma dole ne gwamnatin Nijeriya ta fahimci hakan ta hanyar nuna gaskiya da kuma amincewa da kudurin Dangote na habbaka tattalin arziki.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp