Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kirkirar sarakuna masu darajar ta biyu
A ranar Talata 16 ga watan yuli shekarar 2024 ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar.
SolaceBase rawaito cewa majalisar ta yi karatun farko na kudirin kafin tafiya hutu da tayi wanda suka dawo aiki a makon jiya.
Bayan karatu na biyu da na uku na kudurin, mataimakin shugaban majalisar, Muhammad Bello Butubutu, ya amince da shi tare da zartar da kudurin.
Kakakin majalisar Jibril Ismail Falgore ne ya jagoranci zaman majalisar a ranar Talatar
Sabbin masarautun masu daraja ta biyu da za a kirkiro sun hada da:
1. Masarautar Rano: Rano- Bunkure, Kibiya
2. Masarautar Karaye: Karaye- Rogo
3. Masarautar Gaya: Gaya- Ajingi, Albasu