Majalisar dattawa ta Najeriya ta sauke tare da maye gurbin Sanata Ali Ndume

Majalisar dattawan Nijeriya ta sanar da tsige Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a matsaymin babban mai tsawatarwa na majalisar.

Shugaban majalisar dattawan,Sanata Godswill Akpabio ya sanar da hakan bayan kada kuri’a da ‘yan majalisar dattijan na APC suka amince da tsige Ndume a matsayin babban mai tsawatar wa a majalisar.

An dai maye gurbin Ndume da Tahir Mungono wanda ya ke wakiltar Borno ta Arewa

hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Ndume ke sukar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wata wasika da shugabannin jam’iyyar na kasa na kasa, APmC ta aike wa majalisar dattawa, ta bukaci Ndume ya yi murabus daga jam’iyyarsa ta APC, ya koma kowace jam’iyyar adawa da yake so.

Takardar ta samu sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da kuma sakataren jam'iyyar Barista Ajibola Bashiru.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu masu biyayya ga Tinubu suka kulla makarkashiyar na dakatar da Ndume daga mukamin sa a majalisar.

             

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp