Jaridar Premium Times ta ce ta samu wata wasika daga Majalisar Dokoki ta kasa zuwa ga Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na kasa, Atiku Bagudu, inda ya nemi gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniyar.
Majalisar ta bukaci gwamnati da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar a ranar Alhamis, har sai kwamitin ta ya gudanar da bincike akai.
Sai dai wasikar ta nuna sabanin matsayin majalisar kan yarjejeniyar.
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 9 ga Mayu 2024, kuma Muhammed Argungu ya sanya wa hannu, Majalisar ta bukaci ministan da ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ga kungiyar kasashen Afirka da Caribbean da Pacific da Tarayyar Turai.