Mafi karancin albashi na nairai 70,000 ya razana kamfanoni a Nijeriya
Kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta Nijeriya Organised Private Sector of Nigeria (OPSN) ta bayyana damuwarta kan yadda zata iya biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000, inda ta ce kungiyoyar kamfanoni masu zaman kansu na fama da matsanancin tsadar kayayyaki.
Darakta janar na kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya (NECA), Adewale-Smatt Oyerinde, wanda ya yi magana a madadin kungiyar, ya yabawa gwamnatin tarayya kan amincewa da sabon mafi karancin albashin ma’aikata, inda ya bukace ta da ta sake duba fasalin da zai karfafa wa kamfanoni masu zaman kansu don samun damar biyan albashi.
Sun yaba wa shugaban kasa kan yadda ya yi alkawarin tallafa wa kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu don biyan sabon albashin mafi karancin albashin.
Shugaban NECA ya bayyana cewa, a yayin tattaunawa da kwamitin mafi karancin albashi na kasa, OPS ya nuna damuwarsa kan yadda za ta iya biyan N62,000 da kwamitin bangarorin uku ya ba da shawarar akai.