Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake nada mace a matsayin shugabar ma'aikata ta Najeriya.
Misis Didi Esther Wilson-Jack ta maye gurbin Dr Folashade Yemi-Esan tun daga ranar 14 ga wannan wata na Yuli a cewar sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar.
Sabuwar shugabar ma'aikatan Najeriya ta kasance babbar sakatariya tun a shekarar 2017 kuma ta yi aiki a Ministoci daban daban tun daga wancan lokaci.
Shawarar shugaba Tinubu na sake ɗaukar mace bata rasa nasaba da dokar nan data bukaci a baiwa mata kashi 25 na mukamai a gwamnatin Najeriya wacca shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya tabbatar a zamanin sa