Likitoci sun tsunduma yajin aiki a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria

Likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyar domin matsawa hukuma ta biya su hakkokin su.


Dokta Ashiru Mikail, mataimakin shugaban kungiyar likitoci ta kasa (NARD) reshen asibitin ne ya bayyana hakan a wani taron karawa juna sani a Zariya.


Ya bayyana cewa yajin aikin gargadin ya fara ne da sanyin safiyar Litinin dinnan bayan wa’adin mako guda da aka baiwa mahukunta domin shawo kan lamarin.


Mika'il ce idan ba a yi komai ba bayan yajin aikin na gargadi, kungiyar za ta sake zama domin duba matakin da zata dauka na gaba.


Ya ce bukatun kungiyar sun hada da " biyan albashin mambobin kungiyar GIFMIS wanda ta bukaci a gaggauta biyan wasu sassan albashin likitocin da aka hana a baya.


Ya kara da cewa,ko a watan da ya gabata an rage albashin ‘yan kungiyar da kusan kashi 25 zuwa 27 cikin dari wanda ke nuna daga N58,000 zuwa N60,000.


Ya kara da cewa duk da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi a kasar, babu wani kwakkwaran dalili da hukumar ta bayar na cire kudaden likitocin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp