Kungiyar likitocin Nijeriya ta NMA ta bayyana cewa sabon rahoton baya-bayan nan ya nuna yadda aka gano likitoci da sauran malaman asibiti da aka ce ba su cika karbar cin hanci da rashawa ba a wajen aikinsu sabanin ma'aikatan sauran wasu bangarori.
Shugaban kungiyar na kasa Prof Bala Audu ya bayyana wannan kididdigar a yayin wata zantawa a Abuja.
Binciken kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito ya nuna cewa kusan kaso 30% na mutanen Nijeriya na zuwa neman magani wajen likitoci da sauran malaman asibiti kuma ba su biyan wani cin hanci kuma ba a ma neman su biya wani cin hanci.
Sai dai Prof Audu ya ce kaso 4% ne kacal aka ba da cin hanci ga likitoci da malaman asibiti kuma ya ce za su yi kokarin rage yawan wannan adadin.
Abubakar
ReplyDelete