Kyaftin din kasar Ingila Harry Kane ya bayyana cewa yana da burin lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024.
Gabanin fafatawar su da kasar Sipaniya, dan wasan ya shaidawa jaridar The Mirror cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin sun samu nasara a yau.
Yace a yau idan muka samu nasara,itace nasara mafi girma a tarihi da kuma al'ummar mu
Ya kara da cewa Ina matukar alfahari da zama dan Ingila don haka, babu wani abu da bazanyi ba don samun nasarar kungiyata,don haka a shirye nake tare da 'yan uwana abokan wasa domin mu fafata sossai don samun nasara a wannan wasa.