Kungiyoyin musulmi a Nijeriya sun bukaci gwamnan Sakkwato da ya karfafawa sarkin musulmi gwiwa

Gamayyar kungiyoyin musulmi a Nijeriya (CMON), mai kunshe da kungiyoyin musulmi 33 a fadin kasar nan, sun bukaci Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato da ya karfafawa sarkin musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku gwiwa

Kodinetan gamayyar kungiyar kuma shugaban kungiyar musulmi (MMPN) Alhaji Abdur-Rahman Balogun ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis a Abuja a wani taron manema labarai.


An dai samu cece-kuce dangane da yunkurin gwamnatin jihar Sokoto na tsige sarkin musulmi Sa'ad Abubakar, wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Nijeriya (NSCIA), bayan korar hakimai 15 da gwamnatin jihar ta yi.


Sai dai gwamnatin jihar Sokoto ta ce rade-radin da ake yi na shirin tsige sarkin musulmin ba gaskiya bane .


Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Sambo Danchadi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da ta gabata , ya ce dokar da aka mika wa majalisar dokokin jihar ba ta da wani tanadi na tsige Sarkin Musulmi illa gyare gyare da suke ciki.


Duk da cewa gwamnatin jihar Sokoto ta musanta cewa ba ta shirin tsige sarkin musulmin, kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC), ta ce har yanzu gwamnatin jihar na ci gaba da wannan yunkurin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp