Kungiyar 'yan kasuwar kano ta kafa kwamitoci domin samar da tsaro ga kasuwanni a yayin gudanar da zanga-zanga


Kungiyar 'yan kasuwar kano ta kafa kwamitoci domin samar da tsaro ga kasuwanni a yayin gudanar da zanga-zanga



Kungiyar ‘yan kasuwar Kano ta kafa rundunoni domin samar da tsaro a fadin kasuwanni da wuraren kasuwanci a yayin zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar nan.


Shugaban ‘yan kasuwar Kanon Alhaji Sabi’u Bako,ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani taron gaggawa da wakilan manyan kasuwanni da manyan kantuna na jihar suka gudanar, ya bayyana bukatar daukar kwararan matakai na dakile satar dukiyar jama’a a yayin zanga-zangar.


A yayin taron, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa, Alhaji Bature Abdul Aziz ya kaddamar da kwamitin mutane 20 domin daidaita ayyukan kungiyar 'yan kasuwar


A nasa bangaren, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Balarabe Tatari, ya bukaci matasa da su daina yin ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.


Balarabe Tatari ya ce rahotannin da ke yawo na nuni da cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin lumana, duk da cewa ya zama wajibi su samar da isassun matakan kare Kano a matsayin cibiyar kasuwanci.


Shugaban ya yi ga matasa da su sanya a ransu cewa Kano ce gidansu kuma kar suyi duk wani yunkuri na tada tarzoma.


SolaceBase ta ruwaito cewa Kano cibiyar kasuwanci ce a yankin arewacin Nijeriya, kuma a halin yanzu tana da manyan kasuwanni 8, da kuma shaguna da ke a wurare masu mahimmanci a cikin birni mai kusan mutane miliyan 20.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp