Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Nijeriya (ALGON) ta yaba da hukuncin da kotun koli ta yanke na bai wa kananan hukumomi 'yancin gashin kai.
Shugaban ALGON na kasa Maifata Aminu Mu’azu ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels inda ya yaba da hukuncin wanda yace babban cigaba ne.
A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, Kotun Koli ta umurci Gwamnatin Tarayya ta biya kudaden kai tsaye zuwa asusun kananan hukumomin.
Ta kuma bayyana matakin da gwamnonin jihohi ke yi na rike kudaden kananan hukumomi a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
A cewar shugaban ALGON, wannan ci gaban ya dace a yi farin ciki dashi, musamman ga wadanda ke karkashin kananan hukumomi. ya ce ya kamata a bar kananan hukumomi su yi abin da ya dace ta hanyar yiwa al'umma aiki,ta haka ne za a gane irin tasirin da 'yancin yake dashi ga kowace karamar hukuma a Nijeriya.