Kungiyar daliban Najeriya ta yi kashedin karin kudin makaranta a Ƙasar


Kungiyar daliban Najeriya ta gargadi shugabannin makarantun kasar kan karin kudin makaranta sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na baiwa dalibai rancen kudi.

Wannan gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro na da kungiyar ta fitar a Kano, ranar Laraba wanda Kwamared Okunomo Adewumi ya sakama hannun.

“Duk wata cibiya da aka samu ta kara kudi ba gaira ba dalili, za ta fuskanci fushin Kungiyar dalibai, za mu hada kan mambobinmu tare da daukar kwakkwaran mataki".

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp