Shugaban Najeriya Bola Tinubu yana kan hankalin ƙungiyar kwadago NLC ta yi la'akari da yanayin ƙarfin gwamnati wurin neman mafi ƙarancin albashi.
Tinubu ya ce ya san muhimmancin faranta wa ma'aikata kuma ya san yanayi da suke ciki, amma kuma ya kamata ana sara ana duba bakin Gatari.
Shugaban na Najeriya a wata ganawa da shugabannin kungiyar ta NLC Alhamisɗinnan ya ce gwamnatin sa dau kyautatawa ma'aikata abu mai muhimmanci saboda al'umma baki daya tana amfana da aikin su da ya gudana cikin farin walwala.
A jawaban su yayin ganawar da shugaban kasa shugaban kungiyar kwadago Joe Ajaero ya nuna wa shugaban kasa Tinubu muhimmancin a kara sosai kan abin da ya ke a yanzu, a matsayin mafi ƙarancin albashi, saboda rayuwar tsada da ma'aikata ke fama da ita.