Ku dakatar da zanga-zangar adawa da Gwamnatin Tinubu - APC ta gargadi 'yan Nijeriya


Jam'iyyar APC shiyyar Arewa ta tsakiya ta gargadi matasa da wasu kungiyoyi da ke shirin yin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jam'iyyar ta ce irin wannan shawarar ba za ta yi tasiri ba kuma illa ce ga ci gaban kasar a halin yanzu,  tana mai kira ga masu shirya gangamin da su sake tunani tare da dawo da matasa kan hanyar dai-dai.

Shugaban Jam'iyyar, Alhaji Saleh Mandung Zazzaga, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Jos, babban birnin Jihar Filato, ya ce ya kamata masu kira a gudanar da zanga-zangar su lura da halin da ake ciki a kasar.

Zazzaga ya ce, shugaba Tinubu na kokarin mayar da kasar nan kan turbar ci gaba, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da su mara masa baya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp