Ku ankare, kada ku kusanci wuraren zanga-zanga a Najeriya - saƙon Amurka da Birtaniya da Canada ga 'yan ƙasashen su


Gwamnatocin Amurka, Birtaniya da Canada suna ankarar da 'yan kasashen da su yi taka tsantsan kan zanga-zangar da ake shirin yi ranar ɗaya ga watan Agusta a Najeriya.

Gwamnatocin kasashen uku a wasiku da suka aike ga 'yan ƙasashe masu da ke nan Najeriya sun shawarce su da kada su bari yamutsi ya ritsa da su a yayin da wataƙila rikici zai barke tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga kamar yadda ya faru a baya.

Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da yan kasuwa a manyan biranen Nijeriya ciki har da Abuja suka bukaci tsaurara tsaro a kan dukiyoyin su a yayin wannan zanga-zanga da ya rage ƙasa da awanni 72 ake tunanin za a fara ta.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp