Kotu ta tura tsohon ministan Buhari gidan Yãri


Wata babbar kotu a Abuja ta tura tsohon ministan wutar lantarki Sale Mamman gidan Yãri da ke Kuje kafin a duba yiyuwar bada belin shi, kan zargin da ake masa na almundahana da kuɗin ƙasa, zargin da shi kuma ya musanta.

Hukumar EFCC ta yi ƙarar tsohon ministan tana buƙatar kotu ta bincike shi kan salwantar wasu kuɗaɗen da suka kai sama da Naira biliyan 30.

Lauyan tsohon ministan Femi Ate ya fadawa alkali James Omotosho cewa ya nemi belin wanda ya ke karewa, saidai alkalin ya ce a lokacin wannan zama na sauraron ƙarar bai kai ga samun wannan bukata ba.

1 Comments

  1. Mutum Daya ya saci kudin da ya isa Wani yanki y a yo budget din kanta Allah ya isa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp