Kotu ta bada belin tsohon ministan wutar lantarki kan kudi naira 10bn
Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya a Abuja ya bayar da belin tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman kan kudi naira biliyan 10 da kuma mutum biyu wadanda za su tsaya masa.
An gurfanar da Mamman ne a kan tuhume-tuhume 12 da ke da alaka da hada baki da badakalar kudade.
A yayin da yake yanke hukunci kan neman belin wanda ake kara, Mai shari’a Omotosho ya ce dole ne wadanda za su tsaya masa su mallaki kadarori a Abuja da mafi karancin kudin da ya kai miliyan N750m.
Kotun ta kuma ce dole ne wadanda za su tsaya masa su mika wa kotun takaddun shaidar biyan haraji na shekaru uku.
Kotun ta yanke hukuncin cewa wadanda zasu tsaya masa sai sun mika bayanan banki da fasfo na kasa da kasa ga kotu.
Daga nan ne kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Satumba, 2024, domin a fara shari’ar.