Kira fita zanga-zanga ya sa an kai wani matashi gidan yari a Nijeriya

 Kira fita zanga-zanga ya sa an kai wani matashi gidan yari a Nijeriya 



Rahotanni sun tabbatar sa cewa ana tsare dan Nijeriya mai amfani da shafin Tik tok, Junaidu Abdullahi da aka fi sani da Abusalma a gidan yari bayan ya wallafa wani faifan bidiyo da yake kiran yan kasar da a su shirya domin a gudanar da zanga-zanga kan tsadar rwyuwa a kasar.


Jaridar Daily Nigerian  ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kama Abusalma tun a ranar Laraba kuma daga baya aka kai shi Abuja.


Mustapha Hamza wanda daya ne daga cikin yan'uwan Abusalma ya tabbatarwa da wakilin Daily Nigerian cewa dan uwansa Abusalma a halin yanzu yana a gidan yarin Kurmawa da ke Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp