Kananan hukumomi 8 na jihar Yobe na fuskantar barazanar ambaliya ruwa – NEMA
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta ce rahoton ambaliyar ruwa na shekara ta 2024, AFO, ya bayyana Yobe a matsayin daya daga cikin jihohi 31 da ke da hadarin ambaliya ruwa.
Zubaida Umar, Darakta janar ta NEMA, ta bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da ingantacciyar hanyar kawar da ambaliya na shekarar 2024 a ranar Talatar nan a Damaturu, Yobe.
Zubaida Umar wanda mataimakin daraktan kudi na hukumar ta NEMA, Aminu Ringim ya wakilta, ta kara da cewa hukumar kula da ruwan ta Nijeriya, NIHSA, ta yi hasashen cewa kananan hukumomi takwas a jihar na fuskantar hadarin ambaliya ruwa.
Ta lissafa kananan hukumomin da suka hada da Bade, Jakusko, Yunusari, Gulani, Geidam, Potiskum, Borsari da Karasuwa.
Yace"mun yaba da matakan da gwamnatin jihar Yobe take dauka dan kaucewa ambaliyar ruwa musamman a wannan lokaci".
A nasa bangaren ko’odinetan hukumar a shiyyar arewa maso gabas, Garba Sirajo, ya yi kira ga jama’a da su guji dabi’ar zubar da shara, musamman yadda ake zubar da shara a magudanar ruwa bar kata hakan na kara toshe hanyoyin da ruwa ke bi.