Kamfanin MTN ya sanar da rufe Ofisoshin shi a fadin Nijeriya
Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da rufe dukkan ofisoshi da cibiyoyin da yake da su a fadin kasar nan na tsawon sa’o’i 24, daga ranar 30 ga Yuli, 2024.
Wannan yazo ne daidai lokacin da kamfanin yace wasu fusatattu sun fasa musu kayan amfani a Ofishin su sakamakon rufe musu layuka da aka yi saboda rashin rashin cike tsarin NIN.
Sa'o'i kadan bayan faruwar lamarin, kamfanin na MTN ya ce ya rufe ofisoshinsa a fadin kasar a ranar Talatar nan.
MTN, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na X, ya bukaci abokan hulda da abin ya shafa da su yi amfani da tashoshin su na kafofin sadarwa na zamani don nemam taimako.
Kamfanin ya tabbatar wa abokan huldar sa cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan yau da kullum bayan awa 24.