Ka dena fake wa da Guzuma don ka harbi Karsana - saƙon Ƙungiyar matasa na arewa ga Dele Momodu

Ƙungiyar matasa masu ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya ta arewacin Najeriya da ake ƙira Northern Yoths for Peaceful Coexistence ta yi martani mai zafi ga mawallafin jaridar nan ta Ovation Dele Momodu game da buɗaɗɗiyar wasiƙar da ya tura ga shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Ƙungiyar ta bakin shugaban ta Haruna Bature, ta ce Mawallafin Dele Momodu yana ƙoƙarin yin amfani da wannan wasika ne kawai don cimma wasu muradun sa, saboda bata ga abin da ya haɗa matsalar tattalin arzikin ƙasa da rikicin jihar Rivers ba da har mawallafin ya hade su wuri guda a wannan wasika yana jana hankalin shugaba Tinubu kan su.

Buɗaɗɗiyar wasiƙar Dele Momodun ga shugaba Tinubu dai an wallafa ta ne a wata Jaridar yanar gizo a makonnan.

Ƙungiyar ta ce Dele Momodu ya fake ne da batun tattalin arzikin ƙasar da biyan buƙatar sa kan batun taƙaddamar siyasar jihar Rivers.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp