Shugaban Amurka Joe Biden ya janye daga takarar neman shugabancin kasar a karo na biyu.
Joe Biden ya sanar da hakanne Lahadinnan bayan matsin da ya sha daga 'yan mjalisa na jam'iyar sa ta Democrats su talatin kan ya aje takarar komawa kujerar shugabancin Amurka.
Akwai kuma rahotanni da ke nuna cewa tsohuwar kakakin majalisar wakilai ta Amurka Nanci Pelosi ma ta ƙarfafa wa Biden gwiwar ya aje takardar ta bayan fage.
Wani dalili da ya karfafa ajiye takarar ta Biden shine yadda ya gagara yin magana mai ma'ana sakamakon gigin tsufa a mahawara da aka gudanar na 'yan takarar shugabancin Amurka na shekarar nan ta 2024.
Janye takarar ta Joe Biden ya bar jam'iyar ta Democrats cikin wani yanayi a inda saura wata guda kacal ya rage ta gudanar da babban taron ta, sa'annan watanni biyar suka rage a shiga zabe.
Yanzu dai duk wanda ya maye gurbin Joe Biden zai kara ne da Donal Trump a zaɓen na neman shugabancin Amurka da za'a yi ranar biyar ga watan Nuwamban wannan shekara ta 2024 da muke ciki.