Jigawa ta yi hadin gwiwa da gidauniyar Alfurqan dake Saudi Arabiya don bunkasa tsarin ilimin tsangaya da Alkur'ani
An bayyana hakan ne a lokacin da tawagar gidauniyar karkashin jagorancin shugabanta Sheikh Abdalla Ibn Nasir Al-Utaibiy ta kai ziyara ga gwamna Umar Namadi a ranar juma’a a gidan gwamnati dake Dutse.
Mai magana da yawun gwamnan, Hamisu Mohammad Gumel ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Ya ce Sheikh Al-Utaibiy ya nuna jin dadinsa ga kokarin Gwamna Namadi na bunkasa ilimin kur’ani a jihar Jigawa, yana mai jaddada cewa gidauniyar Alfurqan mai hedikwatarta da ke Ta’if kasar Saudiyya ta sadaukar da kanta wajen tallafa wa alkur’ani, karatu da haddar annic sama da shekaru 50.
Ziyarar a cewar Sheikh Al-Utaibiy da nufin kulla alaka da gwamnatin jihar Jigawa domin inganta hanyoyin koyar da kur’ani ta hanyar samar da dabaru na zamani domin saukaka fahimta da haddace cikin gaggawa, tare da jaddada kwarewar gidauniyar kan hanyoyin koyarwa, wanda ke taimaka wa kurame da yara kanana wajen haddar Alkur'ani.
Gwamna Namadi ya bayyana jin dadinsa da wannan ziyara da kuma alakar da ake kullawa,yace "muna farin ciki da wannan ziyara da kuma kokarin da kuke yi na tallafa mana wajen bunkasa ilimin Alkur’ani, kasancewar ku a nan yana nuna cewa manufarmu daya itace Alkur'ani.
Gwamnan ya godewa gidauniyar bisa kyakkyawar kulawar da tawagar jihar Jigawa ta yi a ziyarar da suka kai garin Ta’if a shekarar da ta gabata.
"Muna matukar godiya da irin karamcin da aka nuna wa tawagarmu a ziyarar da suka kai Ta’if a bara. Irin wannan karamci yana karfafa dankon zumuncin mu da share fagen samun hadin kai mai amfani,”
Daga nan sai gwamnan ya jaddada mahimmancin Alkur’ani a rayuwar al’ummar Jihar Jigawa,yace idan aka yi la’akari da cewa kusan kashi 99% na al’ummarmu musulmi ne, koyarwa da yada koyarwar Alkur’ani mai girma na da matukar muhimmanci, domin ta hanyar wannan littafi ne mutanenmu suke samun shiriya da karfi.
Yace don haka gwamnatin jihar jigawa a shirye take da tayi duk mai yuwuwa wajen kyautata alakar dake tsakani.